
Sanatan Kano ta tsakiya a majalisar dattawan najeriya, Rabiu Musa Kwankwaso ya tallafawa kimanin mutum 3007 da jarin Naira dubu talatin (30,000) kowannensu a yankin mazabar dan majalisar dattawa ta Kano ta tsakiya.
Wadan da suka ci gajiyar wannan tallafi dai sun fito ne daga kananan hukumomin Kano ta tsakiya guda 15 na kwaryar tsakiyar Kano.
Haka kuma, kimanin mata 120 ne suma suka ci gajiyar tallafin jari na Naira dubu 20,000 na matar Shugaban kasa Hajiya Aisha Buhari.