Home Siyasa Sanatan Kano ta Tsakiya: NNPP ta tabbatar da Rufai Hanga ya maye gurbin Shekarau

Sanatan Kano ta Tsakiya: NNPP ta tabbatar da Rufai Hanga ya maye gurbin Shekarau

0
Sanatan Kano ta Tsakiya: NNPP ta tabbatar da Rufai Hanga ya maye gurbin Shekarau

 

 

 

Jam’iyyar NNPP, ta tabbatar da Rufai Sani Hanga a matsayin ɗan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a zaɓen 2023.

Ɗaruruwan jami’an jam’iyyar, daga ƙananan hukumomi 15 da suka haɗa da majalisar dattawa ne su ka tabbatar da Hanga a cibiyar matasa ta Sani Abacha da ke Kano.

Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa Hanga, ya taɓa zama ɗan majalisar dattawa na Kano ta Tsakiya daga 2003 zuwa 2007.

An yi taron tabbatarwar ne, wanda shugaban jam’iyyar NNPP na Kano ta Tsakiya, Abdullahi Zubair ya jagoranta, domin cike giɓin da tsohon gwamnan jihar, Ibrahim Shekarau ya bari.

Malam Shekarau ya bar jam’iyyar NNPP zuwa PDP, bayan wasu rigingimun da ba a kai ga warware wa ba dangane da batun rabon takara a jam’iyyar.

Sai dai babu tabbas ko INEC za ta amince da maye gurbin Shekarau ɗin da Hanga saboda wa’adin maye gurbin ɗan takara da hukumar zabe ta ƙayyade ya wuce.