
Wani rahota ya nuna cewa sanatoci 15 da ‘yan majalisun tarayya 149 basu gabatar da kudurin doka ko guda 1 ba a shekarar farko na majalisa ta 10.
Rahotan, wanda aka fitar a Abuja daga Oke Epia, darakta janar na kula da kudurin da ‘yan majalisa ke gabatarwa, ya yi nuni da cewa, an amince da kuduri 77 cikin 1, 442 da aka gabatar daga watan Yuni na 2023 zuwa Mayu na 2024.
Sanataocin da basu gabatar da kudurin doka ba sun hada da: Amos Yohanna na PDPn Adamawa da Victor Umeh na LP daga Anambra ta tsakiya da Samaila Kaila na Arewacin Bauchi da Abdul Ningi na PDP daga Bauchi ta tsakiya da Ani Okorie na APC a jihar Ebonyi da Adams Oshiomhole na APCn jihar Edo da Neda Imasuen na LP da Kelvin Chizoba na LP daga Enugu.
Sauran sun hada da: Muntari Dandutse na APC daga Katsina ta kudu da Jiya Ndalikali daga PDP a Niger ta kudu da Onyesoh Allwell na PDP daga jihar Rivers da Haruna Manu na PDPn Taraba ta tsakiya da Ahmad Lawan na APC daga Yobe da Napoleon Bali daga Plateau da Abubakar Yari na APC daga Zamfara ta tsakiya.
Binciken Daily Trust ya gano cewa, hudu cikin tsofaffin gwamnoni 13 dake majalisar dattawa da karin sanatoci 21, basu gabatar da kudurin doka ko 1 ba daga watan Yuni na 2023 zuwa Maris na 2024.
Majalisar dattawa ta gabatar da kudurori 475, sai dai guda 19 ne aka amince dasu, yayin da majalisar wakilai ke da kudurori 1, 175 inda aka amince da 58.