Home Labarai Ƴan Sanda da ƴan ƙato-da-gora sun kashe ƴan ta’adda 2 a Katsina

Ƴan Sanda da ƴan ƙato-da-gora sun kashe ƴan ta’adda 2 a Katsina

0
Ƴan Sanda da ƴan ƙato-da-gora sun kashe ƴan ta’adda 2 a Katsina

 

 

 

Rundunar ƴan sandan jihar Katsina tare da hadin gwiwar ƴan ƙato-da-gora sun daƙile wani harin da ‘yan ta’adda a ƙauyen Sabon Dawa da ke gundumar Zakka a Ƙaramar Hukumar Safana.

Gambo Isah, mai magana da yawun rundunar ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a jiya Laraba a Katsina.

A cewarsa, lamarin ya afku ne a ranar Talata, 21 ga watan Yuni da misalin karfe biyar na yamma, bayan da aka samu kiran gaggawa cewa ƴan ta’addar da yawansu ɗauke da bindigogi kirar AK-47 sun kai hari kauyen.

“ Da samun rahoton, sai jami’an ‘yan sanda na yankin Safana su ka yi maza su ka mayar da martani bisa jagorancin Babban Jami’in ƴan sanda na safana inda ya ja tawagar ‘yan sanda da ‘yan banga zuwa yankin.

“Daga nan sai suka yi artabu da ‘yan ta’addan da wata muguwar bindiga, inda suka kashe biyu daga cikinsu tare da dakile wannan mummunan aikin nasu,” inji shi.

Isah ya ce kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Idrisu Dabban ya yabawa ‘yan sanda, ‘yan kungiyar ƙato-da-gora da jama’ar yankin bisa jajircewarsu wajen kare al’umma daga hare-haren ‘yan ta’adda.