Home Labarai SP na ƴan sanda, Daniel Amah ya samu lambar yabo daga Sifeto-Janar bisa ƙin karɓar cin-hanci

SP na ƴan sanda, Daniel Amah ya samu lambar yabo daga Sifeto-Janar bisa ƙin karɓar cin-hanci

0
SP na ƴan sanda, Daniel Amah ya samu lambar yabo daga Sifeto-Janar bisa ƙin karɓar cin-hanci

 

 

 

Wani jami’in ƴan sandan Nijeriya, Daniel Amah ya samu lambar yabo daga Sifeto-Janar na ƴan sandan Nijeriya, Alkali Baba bisa laifin ƙin karɓar cin hancin dala dubu 200 da wasu masu laifi suka yi masa domin a kashe magana.

Amah shi ne baturen ƴan sanda na Caji-ofis ɗin reshen Nassarawa a Kano.

Sifeto-Janar ɗin, wanda mataimakin kwamishinan ƴan sanda mai kula da harkokin mulki a Kano, Abubakar Zubairu ya wakilta, ya ce an karrama jami’in ne saboda yin riƙo da ɗa’a da bin ƙa’idojin aiki, mayar da hankali da sadaukar da kai da kuma nuna kwarewa mai inganci.

Idan dai za a iya tunawa, a watan Afrilun wannan shekara, Amah ya kama tare da bincikar wani Ali Zaki da laifin fashi da makami.

Bayan kama shi, sai Zaki ya bayar da dala 200,000 a matsayin cin hanci ga Amah domin a kashe magana.

Amma dan sandan ya yi watsi da tayin ya ci gaba da bincikensa.