
Wani ɗan sanda mai muƙamin Sajan, mai suna Samson, ya dawo da jakar ajiye kuɗi, wacce a ka fi sani da wallet, ga mai ita a Abuja.
Mai jakar, mai suna Lukman Agbaja ne ya baiyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafin Facebook na Rundunar Ƴan Sanda ta Ƙasa.
Ya ce “ɗan sandan ya tsinci jakar, wacce ke dauke da katin cirar kuɗi, wato ATM da sauran abubuwa masu amfani.
“Sai ya je bankin da na ke ajiya, ya nemi su bashi lambar waya ta. Bayan ya dade ya na neman lambar wayar tawa, da ga bisani sai bankin su ka bashi, shi ne ya kira ni.
“A jiya, 19 ga watan Maris ya dawo min da jaka ta kuma ba a taɓa komai a ciki ba. Sai na bashi tukwici amma abin mamaki, sai ya ƙi karɓa.
“Mutum ne mai kirki da sakin fuska. Ban zaci akwai sauran irin mutanen kirki haka a Nijeriya ba. Dan Allah ku taya ni gode masa,” in ji Agbaja.