Home Labarai Ƴan sanda za su fara kai samame dazuka da gine-ginen da ba kowa a Abuja

Ƴan sanda za su fara kai samame dazuka da gine-ginen da ba kowa a Abuja

0
Ƴan sanda za su fara kai samame dazuka da gine-ginen da ba kowa a Abuja

 

Ƴan sandan Birnin Tarayyar Najeriya Abuja sun fara hai hare-hare dazuzzuka da gine-ginen da babu kowa a cikin gari da unguwannin bayan gari.

BBC Hausa ta rawaito cewa Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Josephine Adeh ne ya faɗi hakan a jiya Laraba, kamar yadda kafar yaɗa labaran Channel ta ruwaito.

A yayin da take ƙaryata jita-jitar cewa akwai mafakar masu garkuwa da mutane a cikin Abuja, ta ce a kwanaki masu zuwa mazauna birnin za su ga an tsaurara matakan tsaro.

Harin ya zo ne ƙasa da sa’a 24 ba bayan da rundunar ƴan sanda ta yi alkawarin za ta fara tattara bayanan sirri da kuma kai samame da ɗaukar sauran matakan tsaro.

“A yau ƴan sandan birnin tarayya sun fara kai hari dazuka da da gine-ginen da ba mutane a ciki a cikin gari da unguwannin bayan gari. Kuma yanzu muka fara,” in ji mai magana da yawun ƴan sanda.

“Mutane za su ga an tsarara tsaro a wurin shige da fice a birnin.”

Ƴa ƙara da cewa duk wanda aka kama za a tantance sa dauki bayanansu sannan a kai su kotu.