Home Labarai Ɗan sanda ya samu ladan N250,000 bayan ya dawo da Dalolin Amurka da ya tsinta

Ɗan sanda ya samu ladan N250,000 bayan ya dawo da Dalolin Amurka da ya tsinta

0
Ɗan sanda ya samu ladan N250,000 bayan ya dawo da Dalolin Amurka da ya tsinta

 

 

A jiya Alhamis ne wata jarida ta yanar gizo mai suna Katsina City News ta bayar da ladan Naira Naira dubu ɗari biyu da hamsin (N250,000) ga wani dan sanda, Nura Mande da ya dawo da dala 800 da ya tsinta na wata hajiya a jihar Katsina.

A tuna cewa wata hajiya ce ta zubar da kudin a sansanin alhazai na Katsina a lokacin da take shirin tafiya kasar Saudiyya don gudanar da aikin bana.

Wani dan majalisar dokokin jihar, Ali Abu-Albaba ne ya mika wa Mande ladan nasa a shelkwatar ƴan sanda da ke Katsina a madadin jaridar.

Abu-Albaba ya ce jaridar ta yanke shawarar karrama dan sandan ne saboda gaskiya da rikon amana.

“Ba kowa ba ne zai iya samun irin wadannan kudaden a wurin da ba wanda ya gani kuma ya mayar wa mai shi.

“Mun ba shi wannan kuɗi da satifiket din ne domin ya karfafa masa da abokan aikinsa da sauran jama’a gwiwa kan rike gaskiya a koda yaushe.

“Da ya dauki kudin, ko da bai mayar da su ba, domin babu wanda ya ke ganin shi, to ai Allah yans ganin shi, sai ya biya a ranar lahira.

“Amma saboda gaskiyarsa da kyawawan halayensa, a yanzu ya kara mutunta kansa da kuma rundunar ‘yan sanda baki daya, saboda mutane da dama sun rika yaba masa,” ya kara da cewa.