Home Labarai Ƴan sanda sun ƙaddamar da bincike kan kisan matashi Khalid Ahmed Bichi

Ƴan sanda sun ƙaddamar da bincike kan kisan matashi Khalid Ahmed Bichi

0
Ƴan sanda sun ƙaddamar da bincike kan kisan matashi Khalid Ahmed Bichi

Rundunar ƴansandan birnin tarayyar Najeriya, Abuja ta ƙaddamar da bincike kan kisan da aka yi wa wani matashi mai suna Khalid Ahmed Bichi.

Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun rundunar, SP Josephine Adeh ta fitar ta ce kwamishin ‘yan sandan birnin ya bayar da uamrnin gaggauta gudanar da bincike domin gano waɗanda suka kashe matashi.

A ranar Juma’a da maraice ne wasu da ba a san ko su wanen ne ba suka harbe matashin a unguwar Maitama da ke birnin tarayyar.

Sanarwar ‘yan sanda ta ambato kwamishinan na tabbatar wa al’umma cewa rundunar za ta yi duk abin da ya kamata domin kamo waɗanda ake zargi da kisan matashin domin gurfarar da su agaban shari’a.

Kisan matashin dai ya ja hankalin al’umma, musamman a shafukan sada zumunta, inda mutane suka yi ta nuna alhininsu da bayyana kaɗuwarsu da kisan da aka yi wa matashin.

BBC Hausa