
Rundunar Ƴan Sanda ta Birnin Tarayya ta ce babu wani harbe-harbe da a ka yi a Gadar Dantata da kuma ‘Ministers Hill’ kamar yadda a ke ta raɗe-raɗi.
Kakakin rundunar, DSP DSP Josephine Adeh ne ya fadi hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba a Abuja.
A cewar sa, wasu kafafen yaɗa labarai ne su ka yaɗa jita-jitar tun a jiya Talata.
Ya ƙara da cewa da samun labarin, rundunar ta tura kwararrun jami’anta zuwa wajen, inda ta gano babu wani harbe-harbe da ya faru a wajen.
“Bayan mun ci gaba da sa ido da fakon ya kin wajen a tsawon dare , gami da bayanan sirri da rundunar ta samu, muna mau shaida wa al’umma cewa labarin kanzon kurege ne kuma ba gaskiya ba ne. Saboda haka jama’a su yi watsi da shi,” in ji shi