Home Labarai Ƴan Sanda sun cafke dagacin da ya haɗa kai da ƴan ta’adda

Ƴan Sanda sun cafke dagacin da ya haɗa kai da ƴan ta’adda

0
Ƴan Sanda sun cafke dagacin da ya haɗa kai da ƴan ta’adda

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina ta kama dagacin kauyen Gobirau da ke Ƙaramar Hukumar Faskari bisa zargin hada baki da ƴan ta’adda.

Kakakin rundunar ƴan sandan, SP Gambo Isah ne ya yi holon dagacin a gaban manema labarai a ranar Juma’a tare da wasu wadanda ake zargin.

Ya ce ƴan sanda sun samu kiran waya na gaggawa cewa an kai wa wani mai suna Yahaya Danbai, ɗan shekara 35 hari a gonarsa da bindiga kirar AK 47.

“amma manomin ya yi kukan kura, ya yi galaba a kan maharin, ya kwace makamin da ke hannunsa ya kuma kashe ɗan ta’addan.

“Ya dauki bindigar AK 47 ɗin da ya kwace ya kai rahoton lamarin ga dagacin, Malam Surajo Madawaki, mai shekara 50.

“Maimakon ya kai rahoto ga ƴan sanda, sai dagacin ya kira wani Hamisu, wanda fitaccen shugaban ‘yan ta’addan ne da aka kashe ya mika masa bindigar AK 47 din aka kwato.

“Saboda haka, Hamisu ya tattara ’yan kungiyarsa, suka kewaye kauyen, suka fito da manomi, suka kashe shi nan take a gaban jama’a,” in ji SP Isah.

Ya kuma ce yan ta’addan sun sanya wa al’umma kudin fansa nera miliyan 10 saboda manomin da ya kashe daya daga cikin ƴan ƙungiyar ne, wanda idan ba haka ba za su kashe kowa a kauyen.

“Tun daga lokacin ne sai dagacin ya gudu ya buya, amma daga bisani sai aka kama shi.

“A yayin da ake gudanar da bincike, dagacin ya amsa laifin aikata laifin,” in ji shi.