
Rundunar ’yan sandan Jihar Nasarawa ta sanar da cafke wani mutum mai shekara 43 bisa zargin yi wa wata gyatuma mai shekara 80 a fyade.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, ASP Ramhan Nansel ya fitar ranar Lahadi a Lafia, babban birnin jihar ce ta tabbatar da kama mutumin.
Sanarwar ta ce an cafke Dan-Asabe Eddo, wanda mazaunin kauyen Kundami ne da ke garin Garaku a Ƙaramar Hukumar Kokona bisa laifin zakke wa gyatumar.
A cewar sanarwar, a ranar 14 ga watan Janairun bana ne aka cafke mutumin wanda ɗan asalin Jihar Kaduna ne amma yana zaune a ƙauyen na Garaku.
“An zarge shi da shiga gidan tsohuwar mai shekara 80, wacce take zaune ita kadai a wannan gida, sannan ya yi mata fyade.
“Bayan sun samu wannan labarin, ’yan sandan da ke ofishinmu na Garaku sun dauki mataki nan take inda suka kama mutumin da ake zargi.”
Sanarwar ta kara da cewa Kwamishinan Ƴan Sanda na jihar, CP Adesina Soyemi, ya bayar da umarni a kai batun sashen binciken masu aikata manyan laifuka da ke Lafia domin gudanar da cikakken bincike a kansa.