
Rundunar Ƴan Sanda a Jihar Niger ta ce ta kama wani Bashiru Abdullahi, wanda a ke zargi kisa da kuma garkuwa da al’umma a Karamar Hukumar Kwantagora.
Kakakin rundunar, Wasiu Abiodun shine ya bayyana haka a wata sanarwar da ya fitar a yau Asabar a Minna.
Abiodun ya ce jami’an sintirin sirri na ƴan sanda ne suka samu nasarar cafke ɗan ta’addan a ranar 14 ga watan Yuli da misalin ƙarfe 4:30 na yamma, inda ta kara da cewa ɗan garin Bangi ne da ke Karamar Hukumar Mariga.
Ya bayyana cewa an kama wanda a ke zargin a Kontagora yayin da ya ke ƙoƙarin hilatar wasu su shiga kungiyar tasa.
Abiodun ya ƙara da cewa da ana tuhumar sa, ɗan ta’addan ya amsa laifukan da inda ya ce shine ma ya ɗauke tsohon ciyaman ɗin Karamar Hukumar Mariga saboda yana bin shi Naira miliyan 5.8.
Abiodun ya ce ana ci gaba da bincike domin kamo sauran ƴan ƙungiyar ta sa.