
Rundunar ƴan sanda a jihar Plateau ta ce ta ceto baturen ƴan sanda, da aka fi sani da DPO na Pankshin, SP Nwapi Augustus, wanda wasu ƴan bindiga su ka yi garkuwa da shi.
Kakakin rundunar ƴan sandan, Alfred Alabo ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi a Jos.
Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya bayar da rahoton cewa, a ranar 11 ga watan Janairu, ƴan bindigar sun yi garkuwa da DPO ɗin tare da guduwa da shi zuwa wani wuri da ba a sani ba.
Alabo, mataimakin Sufeton ‘yan sanda, ya ce biyo bayan sace dan sandan da misalin karfe 8.30 na dare a ranar 11 ga watan Janairu, rundunar, tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro da mafarauta a yankin, su ka kai farmaki, inda a karshe su ka kubutar da shi daga hannun masu garkuwa da mutane.
“An kai jami’in asibiti domin duba lafiyarsa kuma nan ba da jimawa ba za a sada shi da iyalansa,” inji shi.
Kakakin ya ce kwamishinan ƴan sandan jihar, Bartholomew Onyeka, ya tura wata tawagar kwararru domin ganin an cafke wadanda suka aikata laifin tare da gurfanar da su a gaban kotu.