
Rundunar Ƴan Sandan Nijeriya, reshen Jihar Jigawa ta cafke wasu ƴan sane su shida a Ƙaramar Hukumar Haɗeja.
DSP Lawan Shiisu, Kakakin rundunar, shine ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN a yau Asabar a birnin Dutse.
Shiisu ya ce waɗanda a ke zargin ƴan shekara 18 zuwa 25 ne da haihuwa, inda ya ƙara da cewa an damƙe su ne bayan sun yi wa wani Ibrahim Garba satar Naira dubu 13 da wayar salula a ƙauyen Baturiya.
Ya ce waɗanda a ke zargi, mazauna garin Hadejia, sun sacewa Garba kuɗi da wayar ne a kasuwar ƙauyen Baturiya.