
Rundunar ƴan sandan Jihar Anambra ta tabbatar da wani hari da aka kai wa gidan rediyon jihar Anambra, ABS, da sanyin safiyar Litinin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, DSP Toochukwu Ikenga, wanda ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce ba a samu asarar rai ba a lamarin.
Ikenga ya ce wadanda ake zargin ba su samu nasarar kaiwa ga dakin watsa shirye-shirye, amma kuma sun yi nasarar ƙona wasu motoci guda biyu na tashar.
Ya ce, biyo bayan wani kiraye-kirayen da aka yi a yau 30 ga watan Mayu da misalin karfe 4:30 na safiya, na wani hari da a ka kai a gidan rediyon jihar Anambra da ke Idemili ta Arewa, tawagar ƴan sanda da ke sintiri ta mayar da martani cikin gaggawa.
“Amma kuma mun hana ɓata-garin yin kai harin a kan ginin.
“Abin takaici, motoci biyu na aiki mallakar tashar ne abin ya shafa. Ba a rasa rai ba.
“A halin yanzu, an killace tashar kuma ana ci gaba da gudanar da aiki a yankin,” in ji shi.