Home Labarai Ƴan Sanda sun kama ƙasurgumin mai safarar makamai a kan hanyar Abuja-Kaduna

Ƴan Sanda sun kama ƙasurgumin mai safarar makamai a kan hanyar Abuja-Kaduna

0
Ƴan Sanda sun kama ƙasurgumin mai safarar makamai a kan hanyar Abuja-Kaduna

 

 

Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta kama wani da ake zargin mai safarar bindiga ne a yau Laraba a Gusau.

Wanda ake zargin da safarar bindigar mai suna Sa’idu Lawal mai shekaru 41, ya kasance kofur ne a rundunar sojojin Nijeriya.

An kama shi ne a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna ɗauke da bindigu biyu da harsashi da kuma kwanson zuba harsashi guda takwas yayin da yake kan hanyar kai kayan ga wani “abokin ciniki” da ke Gusau.

Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, ya shaida wa manema labarai cewa Lawal sanannen mai garkuwa da mutane ne, ɗan fashi da makami kuma ɗan bindiga ne.

Ya ce an kwato bindiga kirar AK-47 guda daya, AK-49 guda daya, harsashi 200 na alburusai mai girman 7.6mm, harsashi 501 na 7.62x51mm da kuma kwanson jera harsashi takwas da babu komai a ciki a hannun Lawal ɗin.

Shehu ya shaida wa manema labarai cewa, an kama Lawal ne a cikin wata mota kirar Pontiac Vibe mai lamba Legas KRD 686 CY a kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a kan hanyarsa ta zuwa Zamfara.