
A jiya Juma’a ne Rundunar ƴan sandan jihar Akwa Ibom ta yi holon wata mata mai suna Joy Emmanuel mai shekaru 40 bisa zargin shirya garkuwa da mijinta, Emmanuel Ebong.
Kwamishinan ƴan sanda, Olatoye Durosinmi ne ya shaida wa manema labarai cewa, Joy da masu garkuwa da mutane sun karbi kudi naira miliyan 2 a matsayin kuɗin fansa domin a sako mijin nata.
Durosinmi ya ce rundunar ƴan sanda a jihar ba zai gajiya ba har sai rundunar ta kawar da aikata laifuka a jihar.
Da take zantawa da manema labarai, Joy ta ce yanayin kunci ne ya tilasta mata shirin yin garkuwa da Ebong, dan asalin Ntak Obio Akpa a karamar hukumar Oruk Anam.
Ta ce mijin nata ba kawai ya na mata uƙuba da rashin saduwa ba, har ma sauran hakkunanan ta na ciyarwa da sauran bujataunta ya dena sauke mata.
“Dole sai aikatau na ke yi domin na ciyar da ƴaƴa na. Na shirya yin garkuwa da shi ne saboda ina bukatar kuɗi don in kula da kai na da ƴaƴa na.
“Abin takaici, ba a ba ni ma kudin fansar da aka amsa daga mijin nawa ba bayan an yi nasarar sace shi,” in ji ta.
Joy ta ambaci wani Udo Moji, wanda tuni ya tsere, a matsayin jagoran gungun da ya yi garkuwa da mijin nata.
Ta ce: “Sun karbo min kudin kuma ba su ba ni komai ba. Wasu daga cikin ‘yan kungiyar da aka kama sun kashe kudaden shine kuma suka ambaci sunana ga ‘yan sanda.”