
Rundunar ‘yan sanda a jihar Cross River ta kama wani mutum mai shekaru 49, wanda ya kashe, tare da jefa ƴar uwar budurwarsa a cikin tanki.
Rundunar da ke yaki da masu garkuwa da mutane a jihar, karkashin jagorancin Ogini Chukwuma, ta bayyana hakan ga manema labarai a Calabar a jiya Lahadi.
Mista Chukwuma, mai matsyi Sufeto na ‘yan sanda, ya ce wanda ake zargin, Eyo Bassey, wanda a halin yanzu yake tsare, ya amsa laifinsa bayan kama shi da safiyar Lahadi a karamar hukumar Akpabuyo.
Ya ce wacce abin ya shafa, Harmony Edemawan, mai shekaru 45, an bayyana bacewarta tun ranar Alhamis 23 ga watan Disamba.
Chukwuma ya ce an kama wanda ake zargin ne bisa ga sahihan bayanan sirri daga sashin dabarun yaki da garkuwa da mutane.
A cewarsa, wanda ake zargin a baya ya bayar da bayanan karya cewa wacce ya kashe ta sayar masa da gida kimanin Naira miliyan 9 kuma sai ta nemi ta hana shi kudin.
“Don haka ya tuntubi wasu mutane domin su yi garkuwa da ita a wani yunkuri na kwato kudin nasa, amma daga baya ya kashe ta ya kuma jefa ta a cikin wani tanki.
“Mun fito da gawarta daga tankin mai dauke da tare da ajiye ta a dakin ajiyar gawarwaki kuma ana ci gaba da gudanar da bincike domin bankado wasu da suka aikata wannan danyen aikin,” inji shi