
‘Yan sanda a Jihar Plateau sun mayar wa da wani mai suna John Okeke Naira miliyan 5.9 da aka yi masa fashin ta bayan sun kwato masa kuɗin a wurin fashi.
An yi wa Mista Okeke fashi ne a kan titin Jingre-Saminaka, a Ƙaramar Hukumar Bassa ta jihar Filato a ranar 22 ga watan Mayu, inda kuma ƴan sanda su ka mayar masa da kudin da aka kwato a ranar 4 ga watan Yuli.
DSP Alabo Alfred, mai magana da yawun ƴan sanda, a yau Laraba a Jos ya bayyana cewa Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Bartholomew Onyeka ne ya miƙa kudin ga Okeke.
Ya bayyana cewa, a ranar da ake magana, rundunar ‘yan sanda ta Jingre ta samu kiran waya cewa ana yin fashi a unguwar Fuskan Mata da ke kan titin Jingre-Saminaka.
A cewar sa, tuni jami’an ƴan sanda su ka bazama zuwa wajen, inda suka yi musayar wuta da ‘yan fashin sannan su ka ci karfin su.
Ɗaya daga cikin ‘yan fashin ya samu raunin harbin bindiga inda daga bisani ya mutu a asibitin kwararru na Plateau da ke Jos.
Da ganin ’yan sandan, ‘yan fashin su ka ranta s na kare a daidai lokacin da wadanda abin ya shafa, ciki har da Okeke, wanda ke kan hanyarsa daga Saminaka a Jihar Kaduna zuwa Jos, suka kutsa cikin daji.
Daga baya ne a ka gano kudaden Okeke a wurin da aka yi fashin sannan a ka danƙa masa kuɗin sa
DSP Alfred ya bayyana cewa kwamishinan ‘yan sandan ya bukaci mazauna Plateau da su ci gaba da bai wa ‘yan sanda bayanai a kan lokaci da kuma sauran jami’an tsaro domin karfafa yaki da miyagun laifuka.