Home Ƙasashen waje Ƴan sanda 7 sun sha cizo yayin da masu kiwon zuma su kai zanga-zanga a ƙasar Chile

Ƴan sanda 7 sun sha cizo yayin da masu kiwon zuma su kai zanga-zanga a ƙasar Chile

0
Ƴan sanda 7 sun sha cizo yayin da masu kiwon zuma su kai zanga-zanga a ƙasar Chile
Ƴan Sanda a ƙasar Chile sun kama mutum huɗu da ga cikin masu kiwon zuma da bayan da su ka yi zanga-zanga a fadar shugaban ƙasa a Santiago.
Kamfanin Daillancin Labarai na Reuters ya rawaito cewa masu kiwon zumar, a ƙarƙashin ƙungiyar su, sun girke kwangin zuma kusan 60 mai ɗauke da ƙudan zuma kimanin dubu 10 a ciki.
Bayan da su ka fara zanga-zangar ne sai ƙudan zuman su ka fara tasowa, inda su kai kan me-uwa-da-wabi su ka riƙa gasawa ƴan sandan cizo.
Rahotanni dai sun baiyana cewa ƴan sanda 7 ne su ka sha cizon ƙudan zumar, inda saura kuma su ka ranta a na kare.
Farin da ƙasar ta shiga ne tun shekarar 2010 ya shafi noman zuma a ƙasar, sakamakon fulawowi da tsirrai da ciyawu ba sa fitowa saboda rashin ruwa inda kuma su ne abincin da zuma ke ci ta rayu.
Ƴan ƙungiyar sun koka cewa farin na sanyawa kudan zuma na mutuwa kuma yawan su na raguwa, in da su ka nuna cewa mutuwar ƙudan zuma ɗaya, illa ce ga duniya baki daya.
Masu zanga-zangar, waɗanda su ka rufe wasu manyan titunan birnin sun yi kira ga gwamnati da ta farfaɗo da noman zuma domin tattalin arzikin manoman ya dawo.
Sun kuma nemi su gana da shugaban ƙasar Chile, Sebastian Pinera.
A halin yanzu dai, tuni ƴan sanda su ka cafke mutane huɗu a cikin masu zanga-zangar.