
Rundunar ƴan sanda a Jihar Yobe ta tabbatar da mutuwar mutane 10 tare da jikkata wasu da dama a wani hari da mayakan Boko Haram suka shirya a garin Geidam a ranar Laraba.
Kakakin Rundunar, Dungus Abdulkarim, ya tabbatar wa da NAN faruwar lamarin a ranar a yau Asabar a Damaturu.
Ya ce maharan, waɗanda su ka zo a kan babura sun kuma kona gidajen kwana na malaman wata makarantar gwamnati da ke yankin.
“A halin yanzu; al’amura sun dawo daidai kuma jama’a na gudanar da harkokinsu na yau da kullum, yayin da aka tura jami’an tsaro domin yin sintiri da aikin gani da ido domin dakile afkuwar harin nan gaba,” inji shi.
Abdulkarim, mataimakin sufeton ‘yan sanda, ya ce rundunar ta jajanta wa al’ummar Geidam game da harin, inda ya bukaci jama’a da su kai rahoton duk wani motsi da mutane da basu yarda da su ba cikin al’ummarsu ga hukumomin tsaro.