Home Siyasa Ƴan sanda sun tsaurara tsaro gabanin zuwan Buhari domin kamfe ɗin Binani a Adamawa

Ƴan sanda sun tsaurara tsaro gabanin zuwan Buhari domin kamfe ɗin Binani a Adamawa

0
Ƴan sanda sun tsaurara tsaro gabanin zuwan Buhari domin kamfe ɗin Binani a Adamawa

Rundunar ‘yan sanda a jihar Adamawa ta tura karin jami’ai domin tabbatar da ziyarar da shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai jihar an gudanar da ita lafiya lau.

Rundunar ta kuma umarci jami’ai da su nuna kwarewa sosai da kuma mutunta hakkin dan adam.

SP Suleiman Nguroje, kakakin rundunar ‘yan sandan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar a Yola.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa ya bayar da rahoton cewa Buhari zai je jihar a ranar Litinin mai zuwa domin kaddamar da yakin neman zaben ƴar takarar gwamna ta APC, Aishatu Binani.

Ya bayyana cewa ƙarin jami’an sun haɗa da, amma ba’a iyakance ga, masu sintiri na sa ido ba, ƙungiyoyin dabaru / aiki, Rundunar ‘Yan sanda ta Mobile Force, PMF da Runduna ta Musamman ta Yaƙi da Ta’addanci.