
Rundunar ƴan sandan jihar Kano, ta ce ta daƙile wani yunƙurin yin garkuwa da Dagacin Garun-Babba, Abdulmuminu Mudi a Ƙaramar Hukumar Garun-Mallam a jihar.
Kakakin rundunar ƴan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ne ya bayyana hakan ga manema labarai a jiya Laraba a Kano.
“A ranar 9 ga Agusta, 2022, da misalin karfe 01:30, an samu rahoton cewa ƴan bindiga a kan babura, sun yi garkuwa da Dagacin kauyen Garun-Babba a Ƙaramar hu6kumar Garun-Mallam, Abdulmuminu Mudi.
“Bayan samun rahoton, mukaddashin kwamishinan ƴan sandan jihar, DCP Abubakar Zubairu, ya tara tawagar ƴan sanda da kuma rundunar yaki da garkuwa da mutane.
“Tawagar ta samu jagorancin jami’in ‘yan sanda na DPO na reshen Garun-Mallam, CSP Usman Maisoro, da ƴan banga a yankin, domin ceto hakimin kauyen tare da cafke masu laifin,” inji shi.
Kiyawa ya bayyana cewa nan take rundunar ta bazama, inda ta bi sawun wadanda suka aikata laifin.
“Ganin haka ne ya sanya masu garkuwa da mutanen su ka jefar da Dagacin da kuma baburansu uku su ka tsere.
“An ceto Dagacin ba tare da jin rauni ba, inda ƴan sandan su ka kama babura uku da masu laifin ke amfani da su,” inji shi.
Mukaddashin kwamishinan ƴan sanda na rundunar ya yabawa jami’an ‘yan sandan bisa gaggawa da suka yi, sannan ya umarce su da su kara kaimi wajen kamo wadanda ake zargin.