Home Labarai Ƴan Sanda sun kuɓutar da mutane 14 da a kai garkuwa da su a Zamfara

Ƴan Sanda sun kuɓutar da mutane 14 da a kai garkuwa da su a Zamfara

0
Ƴan Sanda sun kuɓutar da mutane 14 da a kai garkuwa da su a Zamfara

 

 

Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta ceto mutane 14 da aka yi garkuwa da su tsawon kwanaki 42 a dajin Kunchin Kalgo da ke Ƙaramar Hukumar Tsafe a jihar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar, SP Muhammad Shehu ya fitar a Gusau a yau Alhamis.

Shehu ya ce an samu nasarar kuɓutar da waɗanda harin ya rutsa da su ne a wani samame da jami’an leken asiri suka gudanar a dajin a ranar Talata.

Ya ce rundunar ‘yan sanda ta gudanar da aikin tare da goyon bayan wasu mutane da ke hada kai da jami’an tsaro domin dawo da zaman lafiya a jihar.

“Rundunar ‘yan sandan ta dauki matakin ne da sahihan bayanan sirri inda suka kai farmaki kan maboyar ‘yan bindigar, inda suka yi nasarar ceto mutane 14 da suka hada da jarirai biyu ‘yan shekara daya kowanne.

“Wadanda abin ya shafa sun sanar da ‘yan sanda cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki kauyukan Nasarawar-Wanke da Rijiya a karamar hukumar Gusau inda suka yi garkuwa da su har tsawon kwanaki 42,” inji shi.

Shehu ya kara da cewa an mika mutanen 14 ga ‘yan uwansu.

Ya ce kwamishinan ƴan sandan jihar Ayuba Elkanah ya yaba da goyon bayan da gwamnati da jama’a ke baiwa ‘yan sanda a kokarin dawo da zaman lafiya a jihar.