
Hukumar kula da harkokin ƴan sanda, PSC, ta sanar da karin girma na musamman ga CSP Daniel Amah, wanda ya ki karɓar cin hancin dala dubu 200, zuwa mukamin mataimakin kwamishinan ƴan sanda, ACP.
Kakakin hukumar, Azuka Ogugua, ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a jiya Juma’a, a Abuja.
Ogugua ta ce hukumar ta PSC ta kuma ba dan sandan kudi naira miliyan ɗaya, a matsayin tukwici da kuma kwarin gwiwa kan kiyaye mutuncin ƴan aikin ɗan sanda.
Shugabar hukumar ta PSC, Mai shari’a Clara Ogunbiyi, mai ritaya ta kotun koli, ta ce Amah ya nuna mutunci da kyawawan halaye da a ka san ɗan sanda da shi.
Ogunbiyi ta ce wannan tukwicin da karin girma na musamman zai zama wani kwarin gwiwa ga dukkan jami’an ƴan sanda su ci gaba da yin abin da ya dace a ko da yaushe a aikin su.