
Alhaji Sani Dangote ya rasu a kasar Amurka bayan ya sha fama da jinya a wani asibiti.
Sani wanda kani ne ga kasurgumin mai kudin nan na Nahiyar Afirka, Aliko Dangote, shi ne mai rike da mukamin mataimakin shugaban kamfanonin Dangote.
Bugu da kari, marigayin shi ne mamallakin kamfanin Dansa Agro-allied Limited.