
A jiya Talata ne Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo Olu, ya kaddamar da wani matsakaicin shirin ginin gidaje a unguwar Victoria Island, wanda zai kara haɓaka yalwar gidaje a jihar.
Shirin mai suna ‘Channel Point Apartments’ wani aikin gidaje ne da aka haɗa tare da haɗin gwiwar Hukumar Rayawa da Kaddarori ta Jihar Legas, LSDPC, da kamfanin Brook Assets and Resources Ltd., mai zaman kansa da ke harkar gina gidaje.
Shirin samar da gidajen, wanda ke a titin Sinari Daranijo, ya kunshi tagwayen gidaje guda 38 masu dakuna biyu da uku a kan fadin kasa murabba’in mita 2,832.
Da yake jawabi yayin kaddamar da aikin, Sanwo-Olu ya bayyana cewa shirin ya zama aikin gina gidaje na 16 da gwamnatinsa ta kammala kuma ta samar a cikin shekaru uku da suka gabata.
Ya ce aikin gidaje guda 38 ya nuna sakamakon hadin gwiwa tsakanin gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu.
A cewarsa, kudurin gwamnati mai ci na samar da gidaje masu araha da inganci ga mazauna, ta hanyar hadin gwiwa da kamfanoni masu zaman kansu ya haifar da sakamako da ake buƙata.