Home Labarai Sarki Sanusi ya ziyarci Kano shekaru 3 bayan sauke shi daga sarautar Kano

Sarki Sanusi ya ziyarci Kano shekaru 3 bayan sauke shi daga sarautar Kano

0
Sarki Sanusi ya ziyarci Kano shekaru 3 bayan sauke shi daga sarautar Kano

A yau Laraba ne dai tsohon Sarki Muhammadu Sanusi II ya kawo ziyara jihar Kano, kimanin shekaru uku da tsige shi a matsayin Sarkin Kano na 14.

Gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje ce ta tsige Sanusi a ranar 9 ga Maris, 2020 bisa zargin rashin biyayya ga gwamnati.

Da farko an kore shi zuwa kauyen Loko da ke jihar Nassarawa inda daga baya aka kai shi garin Awe.

An tsare tsohon Sarkin ne a garin Awe har zuwa ranar 13 ga Maris, 2020, inda kotu ta ce a ba shi yancin sa.

Da ya isa filin jirgin saman Malam Aminu Kano, Malam Sanusi wanda shi ne Jagoran darikar Tijjaniyya a Najeriya ya wuce gidan mahaifiyarsa da ke kan titin Ibrahim Dabo a cikin birnin Kano.

Wata majiya da ke kusa da Sarkin ta bayyana cewa, Sanusi ya sauka a Kano ne a kan hanyarsa ta zuwa Dutse, babban birnin jihar Jigawa, amma ya tsaya a Kano saboda rashin kyawun yanayi.

Majiyar ta ƙara da cewa bayan da wasu masoyan Sarkin su ka ji labarin zuwan na sa, sai su ka garzaya filin jirgin saman Malam Aminu Kano, inda su ka taro shi har zuwa gidan mahaifiyar ta sa.

Daga nan ne ya kwashi gaisuwa ga mahaifiyar ta sa, sannan ya wuce Jigawa.