Home Labarai Sarkin Dutse ya riƙe malamai da matuƙar muhimmanci — Farfesa Sani R/Lemo

Sarkin Dutse ya riƙe malamai da matuƙar muhimmanci — Farfesa Sani R/Lemo

0
Sarkin Dutse ya riƙe malamai da matuƙar muhimmanci — Farfesa Sani R/Lemo

Shararren malamin addinin Muslunci a Kano, Farfesa Sani Umar Rijiyar Lemo ya bayyana cewa marigayi Sarkin Dutse a jihar Jigawa, Nuhu Muhammadu Sanusi, shugaba ne da ya riƙe malamai da matuƙar muhimmanci lokacin ya na raye.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa marigayi Sanusi ya rasu a ranar 1 ga watan Janairu a wani asibiti a Abuja.

Da ya ke isar da saƙon ta’aziyyarsa a yayin karatun tafsiri da ya kae gabatar wa a masallacin Gadon Ƙaya ko wacce Juma’a, Farfesa Rijiyar Lemo ya ce marigayi Sarkin shugaba ne da bashi da girman kai kwata-kwata.

A cewar malamin, lolacin da marigayi Sarkin ke raye, ya ɗauki malaman addinin Musulunci da muhimmanci kuma ya na matuƙar girmama su.

Ya ce Sarkin ba shi da girman kai, inda ya ƙara da cewa duk da yana da sarauta, amma ya na girmama mutane.

“Ko lokacin da ake tafsiri a fadar sa, malamin da ke tafsirin ya gaya min cewa sau uku ke kawai Sarkin ya yi fashi.

“Mutum ne mai tawari’u da masana’antar da kai, Sannan yana matukar girmama malamai da ma al’umma baki ɗaya.

“Mun zubar da hawaye sosai sabo da rasuwar sa. Mu na addu’ar Allah Ya gafarta masa kura-kurensa ya kuma bashi aljanna maɗaukakiya,” in ji Farfesa Sani Rijiyar Lemo.