Home Lafiya Sarkin Kano ya ƙaddamar da gangamin rigakafin korona 

Sarkin Kano ya ƙaddamar da gangamin rigakafin korona 

0
Sarkin Kano ya ƙaddamar da gangamin rigakafin korona 

 

Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya ƙaddamar da gangamin rigakafin cutar korona a Karamar Hukumar Ungoggo a Jihar Kano.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa UNICEF ce ta shirya gangamin rigakafin da haɗin gwiwar Masarautar Kano.
A jawabin sa, Sarkin ya yi kira ga al’umma da su fito a yi musu rigakafin korona da sauran cututtuka, inda ya tabbatar da cewar rigakafin ba ta da wata illa ga jiki.
Ya kuma yi kira da a haɗa hannu guda wajen yaƙi da cutukan da su ke damun al’umma.
Haka ka taron ya haɗa da rigakafin  lafiyar haihuwa da ta yara da sauran shirye-shirye na lafiya a jihar.
Ya kuma nuna alhini kan yadda yara ke fama da cututtuka irin su polio, ƴar lisuwa da kuma matsalolin haihuwa ga mata.
Ya kuma yabawa UNICEF da gwamnatin Kano a bisa kokarin da suke na bunƙasa harkar lafiya a Kano.