Home Labarai Sarkin Lafia ya kori ɗan marigayi sarki a matsayin Ubangarin Lafia

Sarkin Lafia ya kori ɗan marigayi sarki a matsayin Ubangarin Lafia

0
Sarkin Lafia ya kori ɗan marigayi sarki a matsayin Ubangarin Lafia

Sarkin Lafia, Sidi Bage, ya tuɓe rawanin Musa Mustapha Agwai daga sarautar Ubangarin Lafia, nan take.

Ubangarin Lafia shi ne na uku a jerin masu rike da sarautun gargajiya a masarautar Lafia.

A wata sanarwa da sakataren masarautar, Rayanu Isa ya fitar a garin Lafia, ya ce an dauki matakin ne a zaman da majalisar ta yi a jiya Asabar

Mustapha Agwai, wanda ɗa ne ga marigayi Sarkin Lafiya, Mustapha Agwai, an maye gurbinsa da Usman Isa Baba a matsayin sabon Ubangarin Lafia.

A cewar sakataren majalisar, ba a bayar da wani dalili na korar ba, “amma duk da haka, an cire shi cikin gaggawa”.