Home Labarai Sarkin Musulmi ya bukaci Buhari da ya gaggauta ɗaukar mataki kan batun sauyin kudi

Sarkin Musulmi ya bukaci Buhari da ya gaggauta ɗaukar mataki kan batun sauyin kudi

0
Sarkin Musulmi ya bukaci Buhari da ya gaggauta ɗaukar mataki kan batun sauyin kudi

Mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya bukaci shugaban kasar Muhammadu Buhari da ya dauki matakan gaggawa na shawo kan wahalar da jama’a ke ciki a sanadiyyar sauyin kudi domin kauce wa bore.

BBC ya ruwaito cewa Sultan din ya nuna takaicinsa a jiya Litinin kan lamarin inda ya nuna damuwa kan yadda jama’a suka fada cikin yanayi na yunwa da bacin rai saboda canjin kudin.

Matsalar sauytin kudin ta kara tsananta a tsakanin jama’a bayan da rahotanni suka nuna cewa bakuna sun daina ansar tsoffin takardun kudin na naira 200 da 500 da kuma 1,000.

A ranar Laraba da ta gabata ne Kotun Kolin kasar ta hana Babban bankin kasar aiwatar da tsarinsa na hana amfani da tsofaffin kudin a ranar 10 ga watan nan na Fabarairu, har sai ta yanke hukunci a kasar da gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara suka shigar a kan lamarin.

A gobe Laraba ne Kotun Kolin ta ce za ta yanke hukunci a kan karar wadda gwamnonin jihohin uku suka shigar.

Jihohin Kano da Naija da Ekiti da kuma Ondo suma sun bi sahun jihohin uku inda suka shigar da kara a gaban kotun kolin kan batun sauyin kudin.