Home Labarai Sarkin Potiskum ya nuna goyon baya ga sarautar Sarkin Kano Sanusi

Sarkin Potiskum ya nuna goyon baya ga sarautar Sarkin Kano Sanusi

0
Sarkin Potiskum ya nuna goyon baya ga sarautar Sarkin Kano Sanusi

Mai Martaba Sarkin Potiskum Alh. Umar Bubaram Ibn Wuriwa Bauya ya yi mubaya’a ga
Sarkin Kano, Khalifa Dr. Muhammad Sanusi II.

Sarki Bauya ya nuna goyon bayan ne yayin da ya ziyarci Sarki Sanusi a fadar sa da ke Kano.

Wata majiya a masarautar Kano ta shaida cewa Bauya shi ne Sarki na farko da ya ziyarci Fadar Sarki Sanusi tun bayan dawowarsa a karo na biyu.

“in da ya nuna goyon bayan Masarautarsa da fatan Alkhairi ga Sarki.

“Mai Martaba Sarki Muhammad Sanusi ya ce wannan shine nuna soyayya da kauna wacce bazai taba mantawa da ita ba,” in ji majiyar.