
Sarkin Tsaftar Kano, Alhaji Ja’afaru Ahmed Gwarzo ya rasu.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Sarkin tsaftar ya rasu ne a yau Laraba a ƙasar Saudi Arebiya.
Tuni ƴan uwan marigayin su ka tabbatar da rasuwar ta sa ga manema labarai a yau Laraba.
Wata majiya a danginsa ta ce Sarkin tsaftar ya rasu ne sakamakon gajeriyar rashin lafiya a ƙasa mai tsarki, inda ya tafi domin aikin Ummara.
Kafin rasuwarsa, Sarkin shi ne mataimaki na musamman ga Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje kan rigakafin cutar shan Inna, wacce a ka fi sani da polio.