Home Labarai Sarkin Zazzau ya magantu kan zargin ya riƙe chekin N20m na JNI

Sarkin Zazzau ya magantu kan zargin ya riƙe chekin N20m na JNI

0
Sarkin Zazzau ya magantu kan zargin ya riƙe chekin N20m na JNI

 

Sarkin Zazzau, Ahmad Bamalli ya bada dalilan da su ka sanya ya riƙe chekin kuɗi har Naira miliyan 20 na Ƙungiyar Jama’atu Nasrul Islam, JNI.

A tuna cewa JNI, reshen Ƙaramar Hukumar Zaria ta maka Sarkin Zazzau ɗin a kotu bisa zarginsa da karkatar da cekin kuɗi na naira miliyan 20 da ma’aikatar sufuri ta tarayya ta ba ta.

JNI ta ce an biya cekin ne ga kungiyar a matsayin diyyar karɓe filinta na Kwalejin Larabci ta Jama’atu, ɓangaren maza, domin aikin hanyar jirgin ƙasa na Kaduna zuwa Zariya a wani ɓangare na aikin titin jirgin ƙasa daga Ibadan zuwa Kano.

A karar da aka shigar a ranar 25 ga watan Afrilu, a babbar kotun jihar Kaduna, shugaban ƙungiyar da sakataren JNI reshen Zazzau, Zaharadeen Maccido da Usman Maccido, sun bukaci a saki cakin ɗin.

Masu shigar da ƙara sun yi ikirarin cewa sarkin ya rusa shuwagabancin JNI ne a matsayin wata hanya ta rufe musu baki.

Sai dai kuma a wata sanrwa da Wazirin Zazzau, Muhammad Inuwa Aminu ya fitar a jiya Laraba ta ce ta riƙe check-in kuɗin ne domin daƙile rikici tsakanin wasu ɓangarori huɗu a cikin JNI ɗin da ko wannen su ke iƙirarin mallakin kuɗin.

“Mu na sane da labaran da a ke yaɗa wa ta kafafen sadarwa. Mu na yi wa masoya, ƴan uwa da abokan arziki bushara cewa za mu zo da bayanai na gaskiya. Gaskiya za ta yi halin ta.

“Sai dai kuma ya kamata jama’a su sani cewa a kwai ɓangarori huɗu a cikin kungiyar JNI ɗin kuma ko wannen su yana iƙirarin mallakar filin da a ka bada diyyar. Shi ya sa masarauta ta yi maza ta shiga maganar domin samar da zaman lafiya.

“Yanzu mun bari har sai kotu ta ta yi hukunci a kan ƙarar da s ka shigar,”