Home Ƙasashen waje Saudiya ta ƙaddamar da bikin ranar tunawa da kafuwar ta, karon farko tun 1727

Saudiya ta ƙaddamar da bikin ranar tunawa da kafuwar ta, karon farko tun 1727

0
Saudiya ta ƙaddamar da bikin ranar tunawa da kafuwar ta, karon farko tun 1727

 

A yau Talata ne dai Saudi Arebiya, a karon farko a tarihin ta, ta fara bikin ranar tunawa da kafuwar ta kusan shekaru 300 da su ka shuɗe.

Sarki Salman bin Abdulaziz Al Saud ne ya aiyana ranar tun a watan Janairu, za a riƙa yin bikin ranar tunawa da kafuwar ƙasar ne domin tuna sanda Imam Muhammed bin Saud ya kafa gari na farko a Saudiya wato Diriyah, wanda ke arewa-Maso-Yammacin Riyadh a 1772.

An yi bajakolin al’adu daban-daban irin na Saudiya a bikin.

Babban birnin Saudi na farko, lardin Turaif, ya samu tagomashin zama wurin tarihi na da ga UNESCO tun 2010.