
Gwamnatin Saudiyya ta ɗage takunkumin da ta sanya wa Nijeriya na hana ƴan ƙasar shiga ƙasarta saboda annobar korona.
Matakin ya shafi ƙasashen Afghanistan da Afirka Ta Kudu da Namibia da Botswana da Zimbabwe da Lesotho da Eswatini da Mozambique da Malawi da Mauritius da Zambia da Madagascar da Angola da Seychelles da Comoros da kuma Ethiopia, kamar yadda Haramain, wanda ke kula da Masallatai biyu masu daraja na Makkah da Madina ya bayyana.
Wannan na zuwa bayan sanar da ɗage dakatar da Umrah, shekara biyu bayan dakatar da aikin Ibadar saboda annobar korona.
Sannan kuma gwamnatin Saudiya ɗin ta cire duk wasu matakai da ta saka na kariya da ga kamuwa da korona a Masallatan haramin guda biyu.