Home Ƙasashen waje Saudiya ta raba wa mata na’urar jin magana domin jin fassarar huɗuba da yaruka 7 a Harami

Saudiya ta raba wa mata na’urar jin magana domin jin fassarar huɗuba da yaruka 7 a Harami

0
Saudiya ta raba wa mata na’urar jin magana domin jin fassarar huɗuba da yaruka 7 a Harami

 

Babban Ofishin kula da Harkokin Masallatan Harami Guda Biyu ya raba na’urar jin magana 200 ga mata da ba larabawa ba domin jin fassarar huɗuba da yaruka 7 a Masallatan Haramin guda biyu.

Shafin Haramain Sharifain ya wallafa cewa an ɗauki matakin ne domin baiwa mata da ba larabawa ba damar sauraron huɗubar sallar Juma’a da fahimtar ta.