Home Ƙasashen waje Saudiyya ta aiwatar da kisan ƴan ISIS, Alqaeda da sauran waɗanda kotu ta yanke wa hukuncin kisa

Saudiyya ta aiwatar da kisan ƴan ISIS, Alqaeda da sauran waɗanda kotu ta yanke wa hukuncin kisa

0
Saudiyya ta aiwatar da kisan ƴan ISIS, Alqaeda da sauran waɗanda kotu ta yanke wa hukuncin kisa

 

Saudi Arebiya ta sanar da cewa ta ƙaddamar da hukuncin kisa a kan mutum 81 da kotu ta yanke wa hukunci kan laifuka da suka shafi ta’addanci da fyaɗe da kisa, kamar yadda kamfanin labarai na ƙasar SPA ya ruwaito.

Wata sanarwa daga ma’aikatar harkokin cikin gida ta ce daga cikin mutanen akwai mambobin ƙungiyar ISIS da Al-Qaeda da Houthi.

“Mutanen da suka kai 81, an yanke musu hukunci ne kan laifuka daban-daban, ciki har da kashe mutane maza da mata da yara ƙanana,” in ji sanawar.

“Laifukan sun haɗa da shiga ƙungiyoyin ta’adddanci na ƙasashen waje kamar ISIS da Al-Qaeda da Huothi da ke kai hare-hare a cikin ƙasa (Saudiyya) da kuma zuwa wuraren rikici don taya ƙungiyoyin ta’addanci yaƙi.”

Ta ƙara da cewa an kama mutanen ne sannan aka yi musu shari’a a Saudiyya ƙarƙashin jagorancin alƙalai 13 a mataki uku daban-daban na shari’a kan kowane ɗayansu.