
Rundunar ƴansanda a jihar Kano ta cafke wani mutum mai suna Philibus Ibrahim bisa zarginsa da shake budurwar sa mai dauke da juna biyu, mai suna Theresa Yakubu ‘yar shekara 22.
Ibrahim, wanda ya aikata laifin a karamar hukumar Tudun Wada, ya shiga hannu ne tare da wani abokinsa mai suna Gabriel Bila, dukkansu a Unguwar Korau aTudun-Wada.
Kwamishinan ƴansanda na jihar, Mamman Dauda, ya tabbatar da kamun ga wa kamfanin dillancin labarai na ƙasa a yau Talata a Kano.
A cewar Mista Dauda,” a ranar 2 ga watan Afrilu da misalin karfe 4:30 na rana, mun samu labari daga wani bawan Allah cewa an ga wata mata kwance a bakin hanya, a sume a kan hanyar Kano zuwa Jos a kauyen Anadaria.
“Da samun labarin, an garzaya da tawagar ‘yan sanda zuwa wurin, inda aka kai ta babban asibitin Tiga inda likita ya tabbatar da mutuwar ta.
“Bincike, ya nuna cewa wanda aka kashe ya bar Nassarawan Kuki zuwa Kauyen Yantomo da ke Garin Babba LGA a Kano a ranar 27 ga Maris da misalin karfe 6:00 na yamma.
“A yayin da ake gudanar da bincike, an kama babban wanda ake zargin kuma ya amsa laifin da ya aikata ta hanyar amfani da mayafin wanda aka kashe wajen shake ta.
Mista Dauda ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike kuma da zarar an kammala za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu.