Home Labarai Saurayin Fatima Ganduje ya sanya mata zoben lu’ulu’u

Saurayin Fatima Ganduje ya sanya mata zoben lu’ulu’u

0
Saurayin Fatima Ganduje ya sanya mata zoben lu’ulu’u
Isyaka Ajimobi yake sanyawa Fatima Ganduje zoben soyayya

Isiaka Ajimobi, wanda aka yiwa baiko da Fatima Ganduje, ‘yar Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, wanda shima da ne ga Gwamnan jihar Oyo Ajimobi, ya sanya mata wani zoben lu’ulu’u wanda hakan yake nuna cewar shi ne zai aureta.

A tsarin aure irin na Nasara, sanya irin wannan zobe alama ce ta yin aure tsakanin masoya. Ana sa ran dai nan ba da jimawa ba ne za a yi bikin nasu.

Idan ba’a manta ba, a kwanakin baya, Gwamnoni 11 na Najeriya suka zo fadar Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu, domin nemawa Isyiaka dan gidan Gwamnan Oyo auren Fatima Ganduje.

Ba tare da wata-wata ba, Sarkin Kano a matsayinsa na uban ‘ya ya mince da yiwa masoyan baiko.