
Direbobin babur mai ƙafa uku, wanda a ka fi sani da adaidaita-sahu a Jihar Kano sun yi barazanar tsunduma yajin aiki.
Matakin na su ya biyo bayan ci gaba da gudanar da zanga-zangar lumana da suke yi bisa umarnin sauya lambar babur ɗin da hukumar KAROTA ta ba su.
Ko a yammacin jiya Alhamis, matuƙa baburan adaidaita+sahun sun yi cincirindo a bakin gidan tashar Freedom Radio da ke Sharaɗa a birnin Kano domin nuna rashin goyon bayan su ga matakin.
Zanga-zangar dai ta biyo bayan yadda hukumar KAROTA ta ce sai sun biya kudi Naira 8,000 domin sabunta lambar ta su.
Sun kuma koka kan yadda KAROTA ke karɓar kuɗaɗen haraji barkatai a hannun su, musamman ma naira 100 da su ke biya kullum.
A cewar su, ba biyan naira 100 ɗin ne ke damun su ba, wacce su ke biya ta ranar lahadi, duk da cewa jami’an karɓar harajin ba sa fita aiki a ranar, amma a washegari Litinin sai a ce sai su biya har da ta ranar Lahadin.
“Kuma fa har yanzu ba a bamu na’urar nan ta ganin inda mai adaidaita-sahu ya ke ba, duk da cewa mun biya kuɗin tun sama da shekara ɗaya.
“Kullum sai an karbi kuɗaɗe a hannun mu kuma ba ma ganin amfanin kuɗin da mu ke biya,” in ji wani direban adaidaita-sahu.
Da ga ƙarshe, matuƙa baburan sun baiyana cewa da ga lokacin da hukumar KAROTA ta fara kamasu, su ma za su tafi yajin aiki.
A tuna cewa tun a farko-farkon shekarar da mu ke bankwana da ita ne matuƙa baburan adaidaita-sahu su ka tafi yajin aiki sakamakon harajin naira 100 da a ka sanya musu a kullum, inda hakan ya kawo naƙasu a kan al’amuran yau da kullum a jihar.