Home Siyasa Mu Sha’aban Sharada mu ka sani a matsayin ɗan takarar gwamna a Kano — ADP

Mu Sha’aban Sharada mu ka sani a matsayin ɗan takarar gwamna a Kano — ADP

0
Mu Sha’aban Sharada mu ka sani a matsayin ɗan takarar gwamna a Kano — ADP

 

 

Jam’iyyar ADP mai littafi, reshen Kano ta jaddada cewa Shaaban Sharada shi ne ɗan takarar gwamnan Kano tare da yin watsi da ikirarin tsohon ɗan takarar, Nasiru Koguna.

DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa Koguna ya maka Sharada a kotu, inda ya nemi hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa l, INEC ta haramta wa Sharadan tsayawa takara.

Koguna, ta bakin lauyansa, Nasiru Aliyu, SAN, ya ce wakilan jam’iyyar ne suka zaɓe shi bisa ka’ida a matsayin dan takarar ADP a zaɓen fidda-gwani.

Sai dai a cikin wata sanarwa da ta aike wa DAILY NIGERIAN a jiya Asabar, jam’iyyar ta ce Koguna ya yi murabus bisa ka’ida don ba da dama ga dan takara da ya fishi dace wa kuma ya ke da himma.

Jam’iyar ta ce a raɗin kansa Koguna ya janye takarar sa ta hanyar cike fom EC 118 a INEC bayan dawowar Sharada.

ADP ta ƙara da cewa Koguna ya cike duk wasu takardu da ake buƙata domin janye wa da ga takarar, inda ta ƙara da cewa ya ma rubuta wasikar janye war zuwa shugaban jam’iyar na ƙasa.

“Haka ne ya sanya jam’iyar ta miƙa sunan Sha’aban Ibrahim Sharada a matsayin cikakken ɗan takarar gwamna a Jihar Kano, bayan ya cika duk ƙa’idojin da a ke buƙata,” in ji sanarwar da Rabi’u Bako, shugaban jam’iyar a Kano ya sanya wa hannu.