Home Labarai Shahararren mai harkar otal a Kano, Tahir Fadlallah, ya rasu a Lebanon kuma za a binne shi a Kano

Shahararren mai harkar otal a Kano, Tahir Fadlallah, ya rasu a Lebanon kuma za a binne shi a Kano

0
Shahararren mai harkar otal a Kano, Tahir Fadlallah, ya rasu a Lebanon kuma za a binne shi a Kano

 

A safiyar yau Juma’a ne shahararren mai harkar otal da masana’antu, Tahir Fadlallah ya rasu yana da shekaru 74 a Beirut, babban birnin ƙasar Lebanon.

Jaridar DAILY NIGERIAN ta jiyo cewa tun a ranar 15 ga watan Afrilu ne a ka kwantar da Fadlallah a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Clemenceau, inda a ka ajiye shi a sashin kulawa mai zurfi, har kuma ta Allah ta kasance.

A tuna cewa a ranar 23 ga watan Afrilu, 2020, a ka tafi da Fadlallah, wanda shine mai shararren otal ɗin nan mai suna Tahir Guest Palace, zuwa Beirut da ga Kano, bayan da ya kamu da rashin lafiya da a ke zargin cutar korona ce.

Marigayin, wanda ya bar mata ɗaya da ƴaƴa biyar, ya bar wasiyya cewa duk wanda ya rasu, to a binne shi a jihar Kano.

An haifi marigayi Fadlallah a Beirut a shekarar 1948, inda yana ɗan shekara biyu da haihuwa mahifansa su ka dawo Kano da zama.

Har zuwa rasuwar sa, Fadlallah shine Shugaban Ƙwarori Mazuna Nijeriya na Ƙasa.