Home Labarai SHAWARA: Ya kamata gwamnatin Kano ta kafa cibiyar kula da marayu — Na-Ma’aji

SHAWARA: Ya kamata gwamnatin Kano ta kafa cibiyar kula da marayu — Na-Ma’aji

0
SHAWARA: Ya kamata gwamnatin Kano ta kafa cibiyar kula da marayu — Na-Ma’aji

 

Shugaban Jundullah Foundation, Dakta Adam Kamaluddeen Na-Ma’aji, ya yi kira ga gwamnatin Jihar Kano da ta taimaka ta kafa Cibiyar kula da marayu domin inganta rayuwarsu.

Na-Ma’aji ya bayyana hakan yayin da ya ke raba tallafin kayan Sallah da kuɗin ɗinki ga marayu 105 da ke unguwannin Marmara, Sheshe, Alfindiki, Sudawa da kuma Daneji a cikin birnin Kano a jiya Laraba.

Da ya ke jawabi bayan rabon kayan, Na-Ma’aji kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su ƙara ƙaimi wajen tallafa wa marayu da kayan sallah da kuma kula da ilimi da tarbiyyarsu.

A cewar sa, gidauniyar ta ɗauki gaɓarar tallafa wa marayun ne domin koyi da sunnar Annabi Muhammad (S A W) na ta jin ƙan maraya, inda ya ƙara da cewa hakan zai ƙara musu hakuri.

Ya kuma jaddada aniyar gidauniyar wajen ganin ta tallafawa marayu da ke karamar hukumar birni, musamman a wannan wata na Ramadan.

Yace tallafawa marayu da kula da tarbiyyarsu abune da Allah yake farin ciki dashi, a don haka ya bukaci Al’umma da su zage damtse wajan aiwatar da wadannan ayyuka da za su kai bayi zuwa aljanna.

Shugaban Gidauniyar ya buƙaci Gwamnati da masu hannu da shuni da ke cikin al’umma, da su kafa wata cibiya mai karfi wacce zata dinga kula da rayuwar marayu, tare da daukar nauyin karatun su.