Home Labarai Sheikh Kalarawai ya gargaɗi mawaƙan begen Manzon Allah da su riƙa kiyaye kalamai

Sheikh Kalarawai ya gargaɗi mawaƙan begen Manzon Allah da su riƙa kiyaye kalamai

0
Sheikh Kalarawai ya gargaɗi mawaƙan begen Manzon Allah da su riƙa kiyaye kalamai

 

Shahararren malamin addinin Muslunci, Sheikh Tijjani Bala Kalarawai ya ka hankalin mawaƙan begen Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da su riƙa kiyaye kalamai a waƙoƙinsu.

Malamin ya yi gargaɗin me jiya Laraba a Kano, inda ya ce mawaƙa da dama, musamman masu begen Manzon Allah, su na fadar kalaman da ba su dace ba.

A cewar Sheikh Kalarawai, mawakan bege na furta kalamai da ba su dace ba a waƙoƙinsu, inda ya ce hakan na iya kai mutum ga halaka.

Ya yi kira ga mawaƙan da su riƙa tuntuɓar malamai idan za su yi waka domin su saka su a hanya.

“Ina jan hankalin masu wakoki, musamman na begen Manzon Allah, da su kiyaye, su riƙa tuntubar malamai domin su saka su a hanya.

“A gaskiya a na furta wasu kalamai ga Manzon Allah da basu dace ba a cikin wakoki. Ya kamata a samu ilimi sosai kafin a fara bege,” in ji Sheikh Kalarawai