Home Labarai Sheikh Mahi Niass ya naɗa wa Sarki Sanusi rawanin zama shugaban Tijjaniyya na Nijeriya

Sheikh Mahi Niass ya naɗa wa Sarki Sanusi rawanin zama shugaban Tijjaniyya na Nijeriya

0
Sheikh Mahi Niass ya naɗa wa Sarki Sanusi rawanin zama shugaban Tijjaniyya na Nijeriya

 

Babban Halifan Sheikh Ibrahim Niass, Sheikh Mahi Niass, ya naɗa tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ll a matsayin shugaban ɗariƙar Tijjaniyya na Nijeriya a hukumance.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a watan Mayun bara ne dai a ka gaiyaci Sanusi zuwa Senegal, inda a nan a ka sanar da shi a matsayin shugaban Tijjaniyya na ƙasa.

Da ya ke jawabi bayan an yi naɗin na shi a wajen bikin Mauludin Sheik Ibrahim Niass, Sanusi ya yi kira ga al’ummar musulmi da su sadaukar da kansu wajen bin Allah da addu’ar zaman lafiya a kasa.

Ya kuma ci alwashin cewa zai yi aiki tuƙuru domin ci gaban darikar da kuma mabiyan ta.

Sanusi ya kuma yi alƙawarin hada kai da duk wasu masu ruwa da tsaki wajen yaɗa manufofin Tijjaniyya da kuma koyi da shugaban ta Sheikh Niass.