
A yanzu haka wani mutum mai shekaru 51, Usman Madaki ya fara tattaki daga Bauchi zuwa Legas domin murnar nasarar Sanata Ahmed Tinubu da samun tikitin takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar APC a 2023.
Tuni dai Madaki ya isa birnin Ilorin a daren jiya Talata.
Daga bisani Madaki ya bar Ilorin, babban birnin jihar Kwara da safiyar yau Laraba.
Ya shaida wa NAN a Ilorin kafin tafiyar sa cewa duk da cewa bai taɓa haɗuwa da Tinubu ba a rayuwarsa ba, shi dai babban masoyin tsohon gwamnan jihar Legas ɗin ne.
Madaki, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Bauchi ta jihar Bauchi, ya ce ya fara tattakin ne a ranar 10 ga watan Yuni, kuma ya shirya isa Legas ranar Asabar 25 ga watan Yuni.
Madaki ya ce ya gamu da haɗarurruka da dama a kan hanyarsa, ciki har da abin da ya ke zargin yunkurin yin garkuwa da shi a tsakanin Kafanchan da Zangon Kataf.
Ya bayyana cewa har wasu sun yi masa kallon ɗan Boko Haram amma da suka lura shi mutumin kirki ne, sai suka yi masa rakiya zuwa wajen garin bayan sun yo gayya domin su tabbatar da cewa ya tafi.
“Ina son ganawa da Tinubu a Legas domin na taya murna kan nasarar da ya samu a matsayin ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.
“Ina da yakinin cewa zai zama shugaban Najeriya na gaba. Ina son Tinubu, shi ne ubangidana duk da bai san ni ba,”