
Hukumar Kwana-kwana ta jihar Kano ta tabbatar da rasuwar wata yarinya ƴar shekara 4, mai suna Amina Abdullahi Garba bayan ta faɗa cikin rijiya da ke Kofar Waika, daura da Masallacin Karmawi a Ƙaramar Hukumar Ungoggo.
Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Saminu Yusif Abdullahi ya bayyana cewa, hukumar kashe gobara ta Kofar Nasarawa ce ta samu kiran waya na gaggawa da misalin karfe 2:05 na rana, daga wani Alkasim Ibrahim.
Ya ci gaba da cewa da isar su, tawagar ceto ta gano cewa wata yarinya ƴar shekara hudu ta fada cikin rijiya.
“Karfe 14:05 Alkasim Ibrahim ya kawo mana kiran gaggawa”.
Saminu Yusif ya yi nuni da cewa, nan take tawagar ta garzaya, inda ta yi nasarar fito da yarinyar a sume kuma daga bisani jami’an lafiya suka tabbatar da rasuwarta.
Ya ce, an mika gawar Amina ga Hakimin Kofar Waika, Alhaji Isma’ila Yusuf.
“An fito da wanda aka je ceto a sume kuma daga baya aka tabbatar da mutuwar ta, an mika gawar ta ga Hakimin Kofar Waika, Alhaji Isma’ila Yusuf.” in ji shi.